2 Satumba 2020 - 09:46
Ayatollah Khamenei: Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Ha’inci Al-ummar musulmi, Amma Ba Za ta Yi Nisa Ba

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran, Ayatollah Sayyid Aliyul Khamina’i, ya bayyana cewa gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa ko UAE ta kha’inci kasashen musulmi da kuma al-ummar Falasdinu saboda maida huldar jakadanci da Haramtacciyar kasar Isara’ila da ta yi. Sannan ya kara da cewa, wannan halin ba zai da de ba.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a safiyar yau Talata, a lokacinda ya ke jawabi a taron hotunan badiyo da jami’an ma’aikatar ilmi da tarbiyya ta kasa a nan Tehran.

“Lalle wannan halin ba zai dore ba, kuma kunya zaya wanzu a faskar wadanda suka yi watsi da mamayar Falasdinu da kuma falasdinawa, wadanda aka kora daga gidajensu, sannan suka bawa HKI damar fadada ikonta a yankin” in ji jagoran".

Daga karshe jagoran ya bukaci gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa ta farka kafin lokaci ya kure mata, ta kuma yi abinda ya dace.

Dangane da tsarin tarbiyya da ilmi a kasar Iran kuma, Jagoran ya bayyana cewa kasashen yamma sun dage sai sun kutsa cikin tsarin tarbiyya da ilmi na kasashen duniya, musamman na kasar Iran, ta kudurin MDD mai lamba 2030.

Jagoran ya kammala da cewa tsarin tarbiyya, wanda kasashen yamma suke bi a halin yanzu, ya rika ya karye, don baya iya samar da nagartaccen tarbiyan da ake butakata a duniya.

342/